Gwamnatin Najeriya ta yaba da hukuncin da kotun lardin Päijät-Häme da ke ƙasar Finland ta yanke a ranar Litinin, inda ta yanke wa mai fafutikar kafa ƙasar Biyafara Simon Ekpa hukuncin zaman gidan kaso na shekara shida bisa samunsa da laifin ta’addanci.
A wata sanarwa da ministan watsa labarai Mohammed Idris ya fitar, ya ce suna maraba da hukuncin, kuma suna jinjina wa ƙasar ta Finland.
“Hukuncin ya zo a daidai, domin zai zama adalci ga ɗimbin ƴan Najeriya da suka rasa rayukansu da waɗanda suka shiga tashin hankalin a sanaiyar bala’in da su Ekpa suka jefa su,” kamar yadda sanarwar ta bayyana, inda ministan ya ƙara da cewa wannan hukuncin zai ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Finland.
Sanarwar ta ce Ekpa ya yi shekaru yana tunzura jama’a suna aikata laifuka, wanda ke “ruguza rayuwar iyalai da karya kasuwancin su da mayar da yara marayu da jefa garuruwa da dama cikin fargaba, da ma zama silar mutuwar ɗaruruwan mutane da sunan fafutikar da ke barazana ga haɗin kan Najeriya da ƴancinta.”
Ya ƙara da cewa a shirye gwamnatin Tinubu take ta tsayawa da ƙarfinta wajen kare ƴancin ƙasar da mutuncin ƴan ƙasar baki ɗaya ta hanyar “amfani da diflomasiyyar ƙasa da ƙasa da jami’an tsaro da ɓangaren shari’a domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin ƙasar.”