Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya yi kira da a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Rivers inda ya bayyana zaɓen a matsayin “abin kunya da cin fuskar tsarin dimokraɗiyya”.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na X ranar Lahadi.
Atiku ya ce “Yadda aka gudanar da zaɓen ya nuna cewa jam’iyyar APC tana shirin keta doka don samun nasara ta siyasa.”
“Ina jawo hankalin ‘yan Najeriya da ƙungiyoyin duniya da abokan hulɗa kan yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin karkatar da Najeriya zuwa turba mai haɗari,” in ji shi
Atiku ya buƙaci duk jam’iyyun adawa a jihar Rivers su ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, saboda “gwamnatin ba ta da hurumin gudanar da zaɓen.”
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta ce sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata ya nuna cewa jam’iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 yayin da PDP ta samu sauran guda uku.