Hukumar kula da madatsun ruwa ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency (NiHSA) ta yi gargaɗin cewa aƙalla jihohin arewacin Najeriya guda 18 ne ke fuskantar barazanar ambaliya a mako biyu na farkon watan Satumban nan da aka shiga.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce jihohin Najeriya 29 ne tare da Babban Birnin Tarayya Abuja suke fuskantar barazanar ta ambaliya a tsakanin 1 zuwa 15 ga watan Satumba.
Hukumar ta ce ambaliyar za ta iya shafar ƙananan hukumomi 107, da garuruwa 631, sannan aƙalla manyan titunan ƙasar 50 za su fuskanci tsaiko.
Daga cikin jihohin da suka fi shiga barazanar, akwai Borno da Zamfara da Jigawa da Kebbi da Yobe da Filato da Gombe da Taraba da Sokoto, sannan akwai jihar Kaduna barazanar ba ta ƙarfi sosai.