Gwamnatin sojin Burkina Faso ta amince da wata doka da ke haramta neman maza ko luwaɗi a fadin ƙasar, wadda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekaru 5 a gidan kaso, lamarin da ya sa ta kasance ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta samar da wannan doka.
Ƙasashe kimanin 30 a nahiyar Afirka sun haramta ɗabi’ar neman maza, amma Burkina Faso ba ta yi hakan ba gabanin ƙwace mulkin da sojoji suka yi shekaru 3 da suka wuce.
Mambobin majalisar dokokin wucin-gadi da sojoji suka kafa guda 71 ne suka amince da ƙudirin dokar, da aka gabatar.
Read Also:
A jawabin da ya gabatar wa al’ummar ƙasar ta kafar talabijin, ministan shari’a na ƙasar, Edasso Rodrigue Bayala ya ce duk wanda aka kama yana aikata neman maza zai gurfana a gaban alƙali, inda ya ƙara da cewa idan kuma ba dan ƙasa ba ne, za a tasa ƙeyarsa zuwa ƙasarsa.
Dokar na daga cikin dokokin da aka bijiro da su a ƙasar da zummar sake fasalin iyali da tsarin zamantakewar ‘yan ƙasa, kuma za a sanar da al’umma wannan doka ta wajen gudanar da gangami a faɗin ƙasar.
Mali, wadda aminiyar Burkina Faso ce, ta yi wannan doka da ke haramta luwaɗi a watan Nuwamban shekarar 2024.
Ghana da Uganda sun tsaurara dokokinsu da ke yaƙi da ɗabi’ar neman maza a cikin shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya janyo caccaka.