Home General Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi

Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana rana, Juma’a, 12 ga Satumba, 2025, wanda ya yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1447 Ah, a matsayin ranar hutu domin bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Wannan dai na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar ranar Alhamis, wadda ta ce gwamnatin jihar ta bukaci ma’aikata, ‘yan kasuwa da al’ummar jihar su gudanar da hutun cikin lumana tare da yin koyi da Annabi (SAW).

Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen tunani kan darussan hadin kai, juriya da biyayya ga doka.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta ja hankalin jama’a da su yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, ci gaba da bunƙasar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnatin jihar ta kuma taya al’ummar Kano murnar wannan rana mai albarka tare da fatan samun bikin Maulud cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp