Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15

Court

Wata babba kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta yanke wa Mahmud Usman, ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

Mutumin wanda hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar a ranar Alhamis ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ba shi damar mallakar makamai da aikata ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Alƙalin kotun mai shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ajiye Mahmud Usman a ofishin hukumar DSS har zuwa lokacin da za a kammal shari’a kan sauran zarge-zargen da ake masa guda 31.

A lokacin gabatar da ƙarar, an tuhumi Mahmud Usman da Abubakar Abba da aikata ta’addanci a 2022, ta hanyar kai hari kan barikin soji ta Wawa da ke Ka’inji a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Niger, lamain da ya yi sanadiyar kisan mutane da dama.

Ana zargin su da koyon horo a kan sarrafa makamai da haɗa bama-bamai a sansanonin ƴan ta’ada da dama.

Mai shari’a Nwite ya sanya ranar 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a ci gaba da shari’ar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com