Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta janye yajin aikin gargaɗi da ta fara ranar Juma’a sakamakon ƙorafe-ƙorafen da suka shafi rashin kulawa daga ɓangaren gwamnati.

Wata sanarwa da ƙungiyar Nigerian Association of Resident Doctors (Nard) ta fitar ta ce ta janye yajin aikin na kwana biyar ne bayan gwamnatin Najeriya ta amince da fara biyan wasu buƙatunsu.

“Bayan yunƙurin da gwamnati ta nuna na biyan wasu buƙatun da muka sanar, da kuma shirin fara biyan alawus ga ma’aikatan da ke bin bashi…mun amince mu janye yajin aikin daga ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa ta bai wa gwamnatin tarayyar wa’adin mako biyu domin aiwatar da alƙawuran da ta ɗauka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com