NDLEA ta kama Ba’indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a Legas

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta ce ta kama wani ɗan kasar Indiya da wasu mutum uku bisa zarginsu da hannu wajen shigar da ƙwayoyin Tramadol na fiye da naira bilyan uku zuwa cikin kasar.

Hukumar ta NDLEA ta bayyana cewa wannan kamen kwaya shine mafi girma a cikin wannan shekarar da hukumar ta yi, lamarin da ke nuna ƙaruwar safarar muggan ƙwayoyi da ta’ammali da su a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ta ce jami’anta sun yi nasarar kama mutunan ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, sakamakon bin kwakkwafi da bayanan sirri da jami’ansu suka samu.

Hukumar ta ce jami’anta sun gano ƙwayoyin tramol din wadanda aka shigo da su a matsayin magani na multivitamins a cikin wasu walaye, ana ƙoƙari fita da su cikin wasu manyan motoci daga filin girjin.

Rahotanni sun nuna cewa likitoci kan bayar da ƙwayar Tramadol ne don rage radadin ciwo, amma a yanzu tana neman zama wata annoba a tsakanin matasa inda ta ke haddasa mummunan maye.

Bayanai na cewa yawan masu amfani da wannan magani a kasashen Afirka da dama na ƙaruwa duk da illar da take yi lamarin da ke tayar da hankali.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com