Sojojin Najeriya sun cafke kwamandan IPOB

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama Ifeanyi Eze Okorienta, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB mai neman ɓallewa daga Najeriya.

Dakarun sun damƙe kwamandan wanda ake yi wa laƙabi da “Gentle de Yahoo, sun kuma kwato makamai da suka hada da bindigogi kirar Turai da albarusai da kuma kakin sojoji da na ‘yan sanda.

Jama’an tsaron sun bayyana cafke Eze a matsayin wani babban koma-baya ga ƙungiyar ta IPOB da sashen ƙungiyar mai ɗauke da makamai da ke kudu-maso-gabashin ƙasar.

Hakan na zuwa ne makonni bayan wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa wani jagoran ƙungiyar, Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari, bisa samunsa da aikata laifukan ta’addanci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com