Nasarar da Daliban Kano suka Samu a NECO kokarin Ganduje ne – Sanusi Kiru

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi Kiru, ya taya daliban jihar murna bisa nasarar da suka samu a sakamakon jarabawar kammala makarantun sakandare (NECO) na shekarar 2025.

Wannan na zuwa ne bayan da sakamakon jarabar ya nuna yadda daliban jihar suka zama zakaran gwajin dafia darussan Turanci da Lissafi a fadin Nijeriya.

Ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka rabata ga manema labarai, Kiru ya ce wannan gagarumar nasara ba wai kawai tasirin sauye-sauyen gwamnatin mai ci ke nuna wa ba, illa alama ce ta irin jarin da tsohon gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya zuba a bangaren ilimi daga shekarar 2015 zuwa 2023.

“Ingantattun tsare-tsare da aka aiwatar a wancan lokaci wajen gyara makarantu, horas da malamai da samar da kayan aiki su ne tubalan da daliban suka dogara da su wajen kaiwa ga wannan matsayi,” in ji Kiru.

Ya kara da cewa ba adalci ba ne a jingina nasarar kacokan ga gwamnatin yanzu ba tare da la’akari da irin rawar da aka taka a baya ba, domin irin wadannan sakamako na fito ne daga tsare-tsare masu dogon zango.

Sanusi Kiru ya yaba wa daliban da suka yi fice, tare da jinjinawa malamai, iyaye da duk masu ruwa da tsaki da suka bada gudummawa wajen ganin wannan nasara ta tabbata. Ya kuma bukaci gwamnatin mai ci da ta kara dagewa domin ci gaba da inganta harkar ilimi a Kano, domin amfanin al’umma a nan gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com