Wata kotun tafi da gidanka a jihar Kano ta umarci jami’an hukumar dake lura da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano KAROTA da su kasance masu gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon Amana.
Mai shari’a Chief Majistire Halima Wali ce tayi umarnin yayin da take yanke hukunci kan wasu daga cikin mutane 82 da aka kama da laifukan karya dokokin hanya a jihar kano.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada Anipr ya fitar kuma aka raba manema labarai a jihar Kano.
Read Also:
Wadanda aka yankewa hukuncin sun an same su da laifin karya dokokin hanya da suka hadar da sabawa dokar fitilar bada hannu a manyan titunan kwayar birnin jihar.
Kotunan guda biyu da suka zauna a mahadar Kwanar Sabo da ke kan titin zuwa Maiduguri, da kuma Mahadar Mambayya dake gwammaja a jihar kano karkashin jagorancin Mai shari’a hauwa Abba da Mai Shari’a Halima Wali.
Da yake jawabi ga manema labarai Shugaban hukumar ta KAROTA Hon. Faisal Mahmud Kabir ya yabawa Alkalan kutunan bisa jajircewarsu da sadaukarwa da suke wajin tabbatar da an bi dokokin hukumar.
Haka kuma ya tabbatar da cewa hukumar zata samar da dukkan abinda ake bukata domin gudanar zaman kotunan Tafi da gidan ka yadda ya kamata