Gwamnatin Kano ta yi gargaɗi kan zazzaɓi mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini

Hukumar kula da cututtuka ta jihar Kano KNCDC ta fitar da sanarwar gargadi ga ƴan jihar dangane da rahoton da hukumar kula da cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta bayar kan wasu mutane biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar zazzaɓi mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini a Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukan sada zumuntarta. Inda ta ce gargaɗi na daga cikin shirin kare lafiyar al’umma, duba da yadda Kano ke da yawan jama’a da kuma hulɗar kasuwanci da tafiye-tafiye zuwa sauran sassan ƙasar.

Sanarwar ta tabbatar da cewa binciken farko ya nuna waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar ba su da cutar Ebola.

Duk da haka, ana ci gaba da gwaje-gwaje domin gano ko cututtuka irin su zazzaɓin Lassa ko zazzaɓin Dengue ne suka haddasa alamomin da aka gani.

“Cutar zazzaɓin mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini wato ‘Viral Hemorrhagic Fevers’ na daga cikin manyan cututtuka masu haɗari, kuma suna iya bayyana da alamun zazzabi ko amai ko gudawa da kuma zubar jini daga jiki.” in ji KNCDC.

“Waɗannan cututtuka na iya yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane ko kuma daga mutum zuwa mutum ta hanyar jini ko zufa.” hukumar ta ƙra da cewa.

KNCDC ta kuma shawarci jama’ar Kano da “Su kiyaye tsafta ta hanyar wanke hannu akai-akai da sabulu ko abubuwan tsaftace hannu da kauce wa hulɗa da mutanen da ke da zazzabi ko zubar jini ba tare da sanin ko mene ne ba, da kuma gujewa hulɗa da namun daji saboda gujewa kamuwa da cutar.

Haka kuma, ta yi kira da a tabbatar an dafa nama da kyau kafin a ci, sannan a garzaya asibiti idan aka fuskanci alamomin cutar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com