Home Labarai Gwamnan Kano ya tarɓi masu zanga-zangar ƙin kalaman Lawan Triumph

Gwamnan Kano ya tarɓi masu zanga-zangar ƙin kalaman Lawan Triumph

Wasu mazauna birnin Kano a arewacin Najeriya sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW).

Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.

A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa haihwar Annabi da kaciya, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce saboda “ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciyar”.

A cewar malamin, karama na nufin “wani abin al’ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai”. Kazalika, malamin ya ce ruwayoyin ba su inganta ba.

Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin da su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

“In Allah ya yarda za mu ɗauki matakin da bai saɓa wa Shari’a ba,” in ji gwamnan yayin da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi.

“Abin da nake so shi ne ku koma ku rubuto wa gwamna takarda, wadda ita ce za a yi amfani da ita daga nan har zuwa ƙolin ƙoli.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp