Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da karɓo bashi duk da irin gagarumin tagomashin da ta samu na ƙarin kuɗaɗen shiga a ‘yan watannin nan.
Read Also:
A watan Satumbar da muke ciki kaɗai, Najeriya ta samu kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 3 da biliyan 640, ƙarin kashi 411 kenan idan aka kwantanta da Naira biliyan 711 da aka samu a watan Mayu.
Adedeji ya ce ciyo bashi fa ba matsala bane, saboda kafin a ciyo sai da majalisar tarayya ta amince da hakan, haka zalika basa zagayewa su karbo wani bayan wanda aka amince ɗin.
Kalaman na Adedeji, na zuwa ne ƙasa da watanni biyu bayan shugaba Bola Tinubu a watan Yuli ta miƙa buƙatar ciyo bashin Dala biliyan 21 da miliyan 500 daga ƙetare.
Kuma ko a makonni 3 da suka gabata, sai da Tinubu ya ce Najeriya ta samu kuɗaɗen shigar da tayi hasashen samu a shekarar 2025, kafin ma lokacin da tayi tsammani, a don haka bazata dogara da ciyo bashi ba a kasafin kuɗi.