Majalisar Ƙoli ta Ƙasa ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga jihar Kogi, dake yankin Arewacin Tsakiya, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC).
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da sunansa domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya kammala wa’adinsa a watan Oktoba 2025 bayan shafe shekaru 10 a kujerar shugabancin hukumar. Shugaba Tinubu ya ce Amupitan shi ne ɗan jihar Kogi na farko da aka gabatar don wannan mukami, kuma mutum ne da aka sheda baya tsangwama irin ta siyasa.
Farfesa Amupitan, mai shekaru 58 daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, malami ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, inda yake rike da mukamin Mataimakin Shugaban Jami’a (Harkokin Gudanarwa). Ya kware a fannoni da suka haɗa da Company Law, Law of Evidence, Corporate Governance da Privatisation Law. Ya zama Lauya Babban (SAN) a shekarar 2014.
Read Also:
Ya fara karatunsa a Kwara Polytechnic tsakanin 1982 da 1984 kafin ya ci gaba a Jami’ar Jos daga 1984 zuwa 1987. Ya kammala karatun sa na Shari’a a matakin farko a 1988, sannan ya kammala digirin LLM a 1993 da kuma PhD a 2007 a UNIJOS. Har ila yau, ya yi aikin yi wa ƙasa hidima a gidan jaridar jihar Bauchi tsakanin 1988 da 1989.
Baya ga karantarwa, Amupitan ya riƙe manyan mukamai a harkar gudanarwa da harkokin ilimi, ciki har da Shugaban Kwamitin Shugabannin Sassa da Daraktoci (2012-2014), Dekan na Faculty of Law (2008-2014), da Shugaban Sashen Public Law (2006-2008). A halin yanzu, shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Osun.
Ya wallafa littattafai da dama a fannin shari’a, ciki har da Corporate Governance: Models and Principles (2008), Documentary Evidence in Nigeria (2008), Evidence Law: Theory and Practice in Nigeria (2013), da Principles of Company Law (2013).