Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike wa majalisar dattawan ƙasar wasiƙar neman tantance tare da tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, INEC.
Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, Sanata Godswill Akapbio ne ya bayyana haka, yayin da ya karanto wasiƙar Shugaba Tinubu a zaman majalisar na ranar Talata.
Matakin na zuwa ne bayan amincewar majalisar magabatan ƙasar a makon da ya gabata.
Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴanmajalisar su bai wa tantancewar ”muhimmancin gaske”.
Tinubu ya naɗa Farfesa Amupitan ne bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu.