Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Farfesa Joash Amupitan, a matsayin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasar INEC.
Read Also:
Majalisar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Godswill Akpabio ta tabbatar da Amupitan ne bayan kammala tantance shi, inda ya amsa tambayoyin da ƴan majalisar suka yi masa.
Nan gaba kaɗan ne ake sa ran shugaba Bola Tinubu zai rantsar da shi domin kama aiki gadan-gadan.
A ranar 7 ga watan da muke ciki na Oktoba ne tsohon shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban hukumar ta INEC, bayan shafe shekaru 10.
Tun a watan Oktoban 2015 ne marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari ya naɗa Farfesa Mahmoud Yakubu, a matsayin shugaban hukumar INEC, kana ya sabunta naɗin nasa a shekarar 2020.