Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon taya murna ga tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yayin da yake bikin cikar shekarar 69 da haihuwar a ranar 21 ga Oktoba, 2025.
A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da Sanata Kwankwaso ya bayar wajen ci gaban ƙasa ta fannoni daban-daban, ciki har da kasancewarsa Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai a zamanin jamhuriya ta uku da Ministan Tsaro da Gwamnan Jihar Kano sau biyu, da kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa, tasirin siyasar Kwankwaso a Arewacin ƙasar, musamman a Kano, na nuni da irin siyasar jin ƙai da kishin jama’a da ya gada daga marigayi Malam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Sanata Kwankwaso aboki ne kuma abokin aiki wanda muka yi aiki tare a majalisar dokoki ta tarayya a shekarar 1992, sannan muka zama gwamnoni a shekarar 1999. Mun kuma yi aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC. Ko da yake daga baya ya bar jam’iyyar don kafa NNPP, abin lura ne cewa har yanzu yana cikin tafiyar ci gaba,” in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban ƙasa ya yi wa Sanata Kwankwaso fatan alheri, lafiya, da ƙarin shekaru masu amfani ga ƙasa da al’umma.












