Dalilin da ya sa Amnesty ke neman a soke hukuncin kisa a Najeriya

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su soke hukuncin kisa a ƙasar.

Manajar shirye-shirye ta ƙungiyar, Mrs Barbara Magaji ce ta bayyana hakan a Abuja lokacin da take jawabi a taron masu ruwa da tsaki a Ranar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya.

Ƙungiyar ce dai ta shira taron da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Faransa a ƙasar.

Barbara Magaji ta buƙaci a cire dokokin da suka tanadi hukunce-hukuncen kisa daga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma dokokin wasu jihohin ƙasar.

Ta ce ya kamata majalisar dokokin ƙasar ta duba yiwuwar soke hukuncin kisa ga duka manyan laifukan da aka tanadar wa hukuncin a kundin tsarin mulkin ƙasar.

“Babu wata hujja da ke nuna cewa hukuncin kisa na rage aukuwar manyan laifukan”, in ji ta.

A yanzu haka dai jihohin ƙasar 26 da Abuja ne suke da dokokin da suka tanadin hukuncin kisa ga laifukan da suka shafi garkuwa da mutane da fashi da satar shanu da tsafi.

“Duk da tanadin hukuncin kisa a waɗannan jihohin, amma kullum ana ci gaba da samun ƙaruwar irin waɗannan laifukan, musamman garkuwa a mutane da fashi da ma sauran laifukan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com