Babban Ministan tsaron Nijeriya, Alhaji Muhammed Badaru Abubakar, ya murabus.
Wannan na cikin wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta fitar mai dauke da san Hannun Bayo Onanuga wadda ta ce Badaru ya sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu murabus ɗinsa a cikin wasiƙar da ya aika masa, inda ya ce ya yi hakan ne domin samun damar kula da lafiyarsa.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin, tare da gode wa Badaru bisa gudunmawar da ya bayar tun bayan nadinsa a shekarar 2023.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da matsalolin tsaron a Nijeriya su kara dagule wa, duk da cewa jami’an tsaron na sake samun nasarori a yakin da suke yi









