Trump ya nanata aniyarsa ta iya ƙaddamar da hari a Najeriya

Donald Trump ya jaddada cewa Amurka za ta iya tura dakaru Najeriya ko kuma kaddamar da hare-hare domin hana abin ya kira kisan Kiristoci da ake yi.

Ya shaida wa manema labarai cewa ba zai bari a ci gaba da kisan ba.

“Ana kashe kiristoci da dama a Najeriya kuma adadi da yawa, ba zan bari a ci gaba ba.” in ji Trump.

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi maraba da samun hadin kan Amurka wajen yaƙi da mayaka masu tsattsaran ra’ayin addini tare da musanta cewa mayakan sun fi kashe kiristoci.

A watan da ya gabata Amurka ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da take da damuwa da su kan take ƴancin addini.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, Mista Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com