Rikici tsakanin Boko Haram da ISWAP ya yi ajalin mayaƙa sama da

Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa rikicin cikin gida tsakanin ɓangaren Boko Haram da tsagin ISWAP ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mayaƙa guda 200 a tsakaninsu.

Kafar AFP ta ruwaito cewa ricikin ya yi ƙamari ne a tsakanin ɓangarorin ƙungiyar guda biyu a yankin Dogon Chiku da ke gaɓar Tekun Chadi a ranar Lahadi, wanda ya kasance ɗaya daga rigingimu da ya fi zafi saboda bambancin ra’ayi.

“Mun ƙirga aƙalla gawarwaki guda 200,” in ji wani mai suna Babakura Kolo a zantawarsa a AFP.

Wani tubabben ɗan Boko Haram da ke bibiyar harkokinsu da ya ce a kira shi da suna Saddiku ma ya tabbatar da rikicin, inda ya ce, “an kashe aƙalla ƴan ISWAP 200 a rigimar, sannan an kwashe muku makamai da dama, sannan aka kashe ƴan tsagin Boko Haram guda huɗu.”

Ya ƙara da cewa wannan ne rigima mafi zafi da aka yi a tsakanin ɓangarorin mayaƙan guda biyu tun bayan rabewarsu saboda saɓanin fahimta a shekarar 2016.

Wata majiyar tsaro ma ta tabbatar da aukuwar rigimar, inda ta ce “muna da bayanan sirri kan rigimar, kuma mun samu labarin mutuwar mayaƙa sama da 150, wanda kuma labari ne mai kyau a wajenmu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com