Babu sauran sakaci a jam’iyyarmu ta PDP – Kabiru Turaki

Sabon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Kabiru Turaki ya nemi goyon bayan ‘ya’yan jam’iyyar, yana mai cewa “babu sauran sakaci” a jam’iyyar.

Turaki ya bayyana hakan ne a jawabin nasarar da ya yi bayan lashe zaɓen da aka yi yayin babban taron PDP na ƙasa a jihar Oyo ranar Asabar, wanda ya lashe da ƙuri’a 1,516 cikin 1, 834 da aka kaɗa.

“Ina tabbatar muku amanar da kuka ba mu ba za mu ɗauke ta da wasa ba, babu wani sauran sakaci da kuma ƙwace wa ‘yan Najeriya zaɓinsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan zai duƙufa wajen ziyartar dukkan ‘yan jam’iyyar da suke jin ba a yi musu daidai ba tare da tabbatar da adalci ga kowa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com