SAEMA 2025: IMPR Ta kaddamar da Littafi Kan Yaki da Sha da fatauci miyagun ƙwayoyi.
Rukunin Kamfanin Image Merchants Promotion Limited (IMPR), mai PRNigeria, Economic Confidential da Emergency Digest, ya kaddamar da wani sabon littafi da ke dauke da bayanai kan yaki da shigo da kwayoyi da fasa-kwauri a Najeriya.
Umar ya kaddamar da littafin ne a taron SAEMA karo na 7 a hedkwatar hukumar (NDLEA) da ke Abuja, inda aka kuma yi bikin sauye-sauyen da Brigadier General Mohamed Buba Marwa (rtd) ya samar a hukumar.
A jawabin maraba, babban Edita kuma Shugaban Kamfanin IMPR, Alh. Yushau A. Shuaib, ya bayyana cewa sauye-sauyen NDLEA karkashin jagorancin Janar Marwa sun kasance daga cikin canje-canje mafiya ban mamaki a fannin tsaro a Najeriya a wannan zamani.
Ya ce karfafa ayyukan hukumar ya dakile hanyoyin safarar kwayoyi na dogon lokaci, kuma ya dawo da amincewar jama’a ga aikin yaki da kwayoyi.
Shuaib ya kara da cewa a cikin shekaru hudu da suka gabata, Najeriya ta shaida nasarori dakile Safar muggan kwayoyi gami da gurfanar da shahararrun masu laifi, da kuma sauye-sauye a fannin tattara bayanai, horo, da hadin gwiwa tsakanin hukumomi.
Ya kuma jaddada cewa yadda NDLEA ke mai da hankali wajen faɗakar da masu ta’ammali da kwayoyi da wayar da kan jama’a na nuna cewa hukumar na kallon matsalar kwayoyi a matsayin kalubale na tsaro da lafiyar jama’a baki daya.
Sabon littafin da aka kaddamar, mai suna “Anti-Drug, Anti-Smuggling Campaigns: A Corpers’ Chronicle”, Wasu masu hidimar ƙasa mambobin PRNigeria suka rubuta shi, Arafat Abdulrazaq da Tahir Ahmad, wadanda suka kwashe shekarar guda suna rubuce-rubuce kan ayyukan NDLEA da Nigeria Customs Service (NCS).
Aikin su ya hada da bayani kan kai farmaki, kamun kwayoyi, ayyukan wayar da kai, tsaro a kan iyakoki, da kuma sauye-sauyen cikin gida.
Shuaib ya ce dalilin wallafa littafin shi ne saboda aikin bincike mai zurfi, rahotannin bayanai, da kwazo da kwararru da marubutan suka nuna.
Read Also:
Ya kara da cewa littafin ya nuna yadda NDLEA da Customs ke aiki tare, musamman wajen musayar bayanai da gudanar da ayyuka tare domin kawo karshen hanyoyin safarar kwayoyi da laifukan kasa da kasa.
A jawabin sa a wurin taron, Daraktan CISLAC, Mallam Musa Ibrahim Rafsanjani, ya yabawa Janar Buba Marwa kan jagoranci da ya nuna, inda ya ce da nufin siyasa mai karfi, za a iya magance mafi girman kalubalen al’umma.
Rafsanjani ya ce nasarorin yaki da kwayoyi karkashin jagorancin Marwa sun tabbatar da wannan himma.
Ya kara da cewa nadin Marwa a matsayin Shugaban NDLEA ya dace kwarai, saboda jajircewarsa da kokarinsa wajen fuskantar manyan masu safarar kwayoyi da masu amfani da su da daukar matakai masu tasiri da suka sa kasa alfahari.
Shugaban Hukumar gudanarwa na IMPR, Prof. Sule Ya’u Sule, yayin duba littafin, ya yaba wa Alh. Shuaib kan yadda yake goyon bayan matasa ‘yan jarida da kuma nuna musu yadda hukumomin kasa ke aiki.
Ya ce wallafar littafin ya nuna muhimmancin shigar matasa cikin muhawarar tsaro da rubuce-rubuce.
Prof. Sule ya bayyana marubutan a matsayin mambobin hidimar ƙasa masu hazaka, masu gaskiya da daidaito, wadanda ke nuna matsayin kwararru mafi girma.
Ya kara da cewa aikin su ya zo a daidai lokacin da kasa ke fuskantar karuwar amfani da kwayoyi, barazanar kan iyaka, da hanyoyin fasa kwauri
Shugaban Hukumar IMPR ya yaba wa Janar Marwa kan yadda ya sake tsara NDLEA da kuma kara darajar Najeriya a fagen yaki da kwayoyi a duniya.
Ya ce sabuwar aminci da sahihanci na NDLEA ya samo asali ne daga jagoranci mai karfi da sauye-sauyen da ke nuna gaskiya da sakamako mai kyau.
A madadin marubutan biyu, Arafat Abdulrazaq ya gode wa shugabannin IMPR kan tallafi, shawarwari, da yanayi mai kyau da suka basu a shekarar aikin su.
Ya ce rubuta littafin ya fadada fahimtarsu kan sadaukarwar jami’an NDLEA da Customs.
Ya gode wa iyalai, abokan aiki da manyan jami’an su kan goyon baya, inda ya ce littafin ba wai kawai tarin rubuce-rubuce ba ne, amma gudunmawa ce ga cigaban kasa.
Ya sadaukar da littafin ga jami’an tsaro dake fuskantar barazanar kwayoyi da fasa-kwauri tare da fatan littafin zai kara wa matasan Najeriya sha’awar shiga harkokin kasa da bada gudunmawa mai ma’ana.
PRNigeria










