Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya, wannan mataki na zuwa ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya.
A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro.
takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da kuma kauce wa duk wata barazana.
Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da waɗanda ke Zariya, Daura, Sakkwato, Potiskum, Ikare-Akoko, Abaji, da sauransu.










