Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta ce aƙalla mutum 227, ciki har da ɗalibai 215 da malamai 12 ƴanbindiga suka sace lokacin da suka kai hari makarantar St. Mary da ke garin Papiri a jihar Neja.
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta CAN reshen jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya fitar ya ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin ɗimuwa da kaɗuwa.
Da tsakar daren ranar Alhamis ne wasu mahara ɗauke da makamai suka far wa makarantar – wadda ta kwana ce, da ta ƙunshi furamare da sakandire – tare da sace ɗaliban, bayan da suka harbi maigadi.
Gwamnatin jihar Neja ta ce sai da bayar da umarnin rufe duka makarantun yankin sakamakon samun bayanan sirri kan barazanar tsaro, amma makarantar ta yi gaban kanta wajen buɗewa tare da ci gaba da karatu ba tare da neman izini ko sanar da gwamnati ba.
Harin na zuwa ƙasa da mako guda da wasu ƴanbidiga suka sace ɗalibai mata 25 a makarantar sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi mai maƙwabtaka.
Tuni dai gwamnatin ƙasar ta ce ta baza jami’an tsaro domin kuɓutar da duka ɗaliban.









