Rahotannin daga jihar Filato na bayyana cewa Ma’aikatar ilimi ta jihar ta bayar da umarnin rufe duka makarantun jihar na furamare da sakandire sakamakon ƙaruwar matsalar satar ɗalibai a ƙasar.
Hukumar Ilimi a matakin farko ta jihar, PSUBEB ta bayyana ɗaukar matakin a matsayin matakin kariya ga ɗaliban jihar.
Matakin na zuwa ne bayan sace ɗaliban sakandiren Papiri a jihar Neja, kwana biyar bayan sace ɗalibai 25 na makarantar ƴanmata a jihar Kebbi.
Ma’aikatar ilimin jihar ta ce matakin na wucin-gadi ne kuma ya zama dole, la’akari da halin da ake ciki.
Cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta buƙaci duka masu ruwa da tsaki a harkar makarantu su yi biyayya wa umarnin.
Matakin ya shafi duka makarantun sakandire na ƙananan sakandire da na furamare.









