Home Labarai Dalibai 24 da ‘yan bindiga suka sace a Kebbi sun shaƙi iskar...

Dalibai 24 da ‘yan bindiga suka sace a Kebbi sun shaƙi iskar ‘yanci

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar ceto ɗalibai mata 24 da ‘yan bindiga suka sace a makarantar sakandiren Maga dake jihar Kebbi a makon da ya gabata.

A ranar 17 ga watan Nuwamba da sanyin safiya ne ‘yan bindigar su ka kai hari makarantar tare da yin garkuwa da ‘yan matan, ‘yan sa’o’i bayan barin dakarun ƙasar daga yankin.

Harin na Kebbi ya ta’azzara matsalar tsaro a Najeriya, inda wasu mahara na daban suka afkawa yankin Eruku na Kwara tare da sace masu ibada kodayake an samu nasarar ceto dukkaninsu.

Haka zalika, Ƙungiyar Kiristocin Najeriya ta ce 50 daga cikin ɗalibai fiye da 300 da ‘yan bindiga suka sace a makarantar Katolika dake Neja sun shaƙi iskar ‘yanci.

Shugaba Tinubu ya yabawa jami’an tsaron ƙasar da ƙoƙarin da su ke yi, tare da kira na su jajirce don ceto suaran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp