Home General KAROTA ta bukaci Al’ummar jihar Kano su bawa jami’anta hadin kai

KAROTA ta bukaci Al’ummar jihar Kano su bawa jami’anta hadin kai

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar Kano KAROTA ta bukaci direbodin jihar da su zamo masu bin doka da oda, a dukkan lokacin da suke kan titunan jihar.

Mataimakin shugaban hukumar Auwal Lawan Aranposu ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar kautar girmamawa da kungiyar shuwagabannin kungiyar direbobin mota ta NURTW shiyyar kano ta kadu ta bashi a dakin taro na hukumar KAROTA dake kano.

Auwal Aranposu ya yabawa kokarin kungiyar na yadda suka ga dacewar bashi wannan kyautar girmama akan yadda yake gudanar da ayyukansa a hukumar.

“Yau ina cike da farin ciki, saboda a ko da yaushe kana gudanar da aikin ka tsakaninka da Allah ba domin wani ya yaba maka ba, sai dan ka sauke nauyin da ke wuyanka, kuma kana gwada adalci da jajircewarka akan aikin dake gabanka, kai dai kasan kan yi ne tsakani da Allah.”

“Ni bana karbar takardar girmama, idan aka ce za’a karramani nakan ce a bari sai na bar kujerar, anan ne za’a gane cewa na cancanta ko kuma akasin haka”

“Amma a dukkan abin da aka lisafta a wannan waje nasan abubuwa ne da idan an yaba min sakamakon yin su na tabbatar da cewa kwarai na aikata su domin ganin an sami gobe mai kyau a harkokin sufurin jihar kano.”

Da yake jawabi tun da fari Shugaban kungiyar shuwa

gabannin kungiyoyin direbobin mota ta NURTW shiyyar kano ta kadu Musa Mika’il, ya yabawa Auwal Aranposu bisa yadda yake kokari wajen kari martaba da mutuncin direbon dake yankin Kano ta Kadu dama jihar kano baki daya.

“Mai girma DMD bazan cika ka da zance ba ina, illa iyaka an sake mika godiyar mu kan yadda kake kare mutuncin direbobin mu, wannan ce ta sanya a madadin su muka ga dacewar karrama ka da wannan lamba ta girma”. Taron ya sami halartar daukacin shuwagabannin kungiyar shuwagabannin direbobi ta NURTW shiyyar kano ta kadu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp