Home Labarai Atiku Abubakar ya magantu kan ceto Daliban Kebbi

Atiku Abubakar ya magantu kan ceto Daliban Kebbi

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Ƙasar kan ceto ɗalibai mata da aka sace a Kebbi da aka yi a baya bayan nan.

Ya ce sako su ba abin da za a gabatar da shi a matsayin nasara ba ne, illa wani abu da ke nuna yadda tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya wallafa a yau Laraba, ya ce ”lamarin na sake tunatar da al’umma ne cewa ƴan ta’adda na cin karensu babu babbaka a ƙasar, ita kuma gwamnati ta ɓige da sanarwa”.

Jawabin nasa na zuwa ne a matsayin martani game da kalaman mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, a wata hira da ya yi, inda ya ce hukumar tsaro ta DSS da sojoji sun gano inda masu garkuwa da mutanen suke, suka tuntuɓe su kuma aka kai ga nasarar cimma sako yaran ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Ya kuma ce bayan jami’an tsaron sun samu bayanan, ba su kai musu hari ba saboda fargabar kar abin ya rutsa da fararen hular da ke hannunsu.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi watsi da hujjojin, inda ya ɗiga ayar tambayar kan ‘Me ya sa gwamnati ke tunƙaho da tattaunawa da ƴan ta’adda maimakon hallaka su? Kuma me ya sa ba a kashe kowa ba ko a kama wasu ko kuma a ruguza maboyar su?”

Atiku ya kuma ƙara da cewa bayanan da gwamnatin ta fitar na nuna cewa ƴan ta’adda da ƴan bindiga sun zama kamar wata gwamnati mai zaman kanta da ke yarjejeniya, su karɓi kuɗin fansa, su kuma koma cikin daji daga baya su sake sace wasu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp