Home Labarai Tinubu ya umarci jami’an tsaro su yi wa dazukan Kwara da Kebbi...

Tinubu ya umarci jami’an tsaro su yi wa dazukan Kwara da Kebbi ƙawanya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su tura jami’an da za su zagaye dazukan jihohin Kwara, Kebbi da kuma wasu yankuna na Neja , bayan ƙaruwar ayyukan masu riƙe da makamai a yankunan.

Shugaba Tinubu ya kuma ce, dole ne sojojin sama su kasance suna sanya idanu sosai ba dare ba rana a waɗannan yankuna domin taimakawa sojojin da ke ƙasa aiwatar da ayyukansu cikin sauki.

Umarnin Shugaban ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar taɓarɓarewar rashin tsaro a tsakiyar arewa da Arewa maso Yamma, ciki har da sace masu ibada a Eruku da ke Jihar Kwara, da kuma jerin hare-haren da aka gani a sassan Kebbi da Neja da ta kai ga sace ɗalibai, abin da ya haifar da damuwa a sassan ƙasar da ke yammacin Afirka.

Duk da cewa an samu nasarar ceto mutane da dama, hukumomin tsaro har yanzu na aiki tuƙuru domin ‘yantar da wasu da ake kyautata zaton suna tsare a cikin dazuzzuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp