Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Najeriya, ta bankaɗo muggan ƙwayoyi da aka ɓoye a wasu manyan ɗakunan ajiyar kayayyaki da kuɗinsu suka tasama sama da naira biliyan shida da miliyan 700 a jihar Lagos.
Wata sanarwa da daraktan sashen yaɗa labarai na hukumar, Femi Babafemi ya fitar tace, yayin samamen da jami’an NDLEA ɗin suka gudanar, sun kuma cafke wani babban dillalin ƙwaya mai suna Onyekachi Pius tare da wasu mutum biyar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ci gaba da cewa, an samu mutanen da aka cafke ɗauke da waɗannan ƙwayoyi a tattare da su, bayan samamen da aka kai maɓoyarsu da ke wani rukunin gidajee da ke Lagos.
Daga cikin kayayyakin da aka gano a hannun su, akwai maganin Tramadol da kuma kodin, wanda ake zargin sun adana ne saboda bikin Kirismeti da ke ƙaratowa.
A cewar NDLEA, manyan motoci aka yi amfani da su wajen fitar da tarin waɗannan muggan ƙwayoyin daga rukunin gidaje na Festac da ke yankin Apple Junction.












