Home Labarai Gwamnatin jihar Kebbi ta damka daliban da aka kubutar hannun iyayensu

Gwamnatin jihar Kebbi ta damka daliban da aka kubutar hannun iyayensu

Gwamnatin jihar Kebbi ta mika daliban makarantar ‘yan mata ta Maga da aka kubutar daga hannu ýan bindiga su 24 ga iyayensu.

Wannan dai ya gudana ne bayan wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar, wanda yake cike da adduóin neman zaman lafiya da ingantaccen tsaro a birnin kebbi, wanda gwamantin jihar ta shirya domin sake hada yaran da iyayen nasu.

Bikin ya gudana ne karkashin kulawar kwamishin ilimi ta jihar Hajiya Halima Bande, wadda ta nuna damuwarta bisa halin da yaran da iyayen su suka shiga na tashin hankali.

Da take jawabi a wajen taron matar gwamnan jihar Hajiya Zainab Nasare Idris ta bukaci iyayen yaran da kada wannan dalilin yasa su yi watsa da yin karantun ‘ya’ya mata wanda hakan ka iya mayar da hannun agogo baya.

A makon jiya ne aka tashi da labarin cewa ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi awun gaba da ɗaliban sakandiren Maga su 25 a yankin  karamar hukumar Danko-Wasagu da ke jihar Kebbi, inda suka kashe mutum biyu a makarantar.

Ana tsaka da jimamin satar ɗaliban kwatsam sai aka tashi kuma da labarin garkuwa da ɗalibai sama da 250  a makarantar sakandiren St Mary da ke garin Kwantagora na jihar Neja.

Baya ga waɗannan, masu ɗauke da makaman sun gudanar da mabanbantan hare-hare tare da awun gaba da mutane a jihohin Kwara da Sokoto da kuma Kano.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp