Home Labarai Tinubu ya ƙara yawan sabbin ƴansandan da za’a ɗauka zuwa 50,000

Tinubu ya ƙara yawan sabbin ƴansandan da za’a ɗauka zuwa 50,000

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa dokar ta ɓaci a ɓangaren tsaro, inda ya buƙaci ɗaukar sabbin sojoji da ƴansanda domin inganta harkar tsaron.

Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta sanar, mai ɗauke da sanya hannun Bayo Onanuga, ta ce shugaban ya bada umarnin ɗaukar ƙarin sabbin ƴansanda 20,000, wato ƙari a kan 30,000 da ya ce a ɗauka a makon jiya, abinda ya kawo sabon adadin zuwa 50,000.

Tinubu ya kuma bada umarnin amfani da wuraren horar da sabbin jami’an da za’a ɗauka a cibiyoyin horar da masu yiwa ƙasa hidima na NYSC, baya ga cibiyoyin horar da ƴansandan da ake yiwa gyarar fuska domin inganta su.

Sanarwar ta ƙara da cewar, za’a sake horar da jami’an ƴansanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗansandan gada gadan.

Shugaban ƙasar ya kuma bada umarni ga hukumar tsaron farin kaya ta DSS da ta gabatar da mutanen da aka yiwa horo a matsayin dakarun Gandun Daji domin fara aiki nan take, domin kawar da ɓatagarin da suka mamaye wasu dazukan ƙasar.

Tinubu wanda ya bayyana matakin a matsayin na dokar ta ɓaci, ya ce za su ɗuki duk matakan da suka dace wajen baza jami’an tsaro a ko ina, musamman yankunan da ake fama da matsalar tsaro domin tinkarar rikicin kai tsaye, ta yadda za su hana bacci ga duk wani ɗan ta’adda.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika dake jihar Neja.

Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.

Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ƴansanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.

Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Mujami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.

Shugaban ya kuma jajantawa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp