Home Labarai Tinubu ya yi ta’aziyyar Sheik Dahiru Bauchi

Tinubu ya yi ta’aziyyar Sheik Dahiru Bauchi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin.

Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa.

Shugaban ya ce rasuwar shehin malamin rashi ne ga ƙasar baki ɗaya, ba ga iyalansa da ɗalibansa ko mabiyansa kaɗai ba, inda ya ƙara da cewa har yanzu yana tuna irin ƙarfafa gwiwar da marigayin ya ba shi a lokacin da ake shirin zaɓen 2023.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya babba da ke amo sosai,” in ji shi shugaban, sannan ya bayyana shi da hadimin Qur’ani kuma malamin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa za ta bar babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban.

Tinubu ya yi ta’aziya ga mabiya shehin a faɗin Najeriya da ma ƙasashen waje, sannan ya yi kira gare su da su yi koyi da halayensa na gari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp