Sojojin Nijeriya sun kubutar da Yara mata 12 daga hannun mayakan ISWAP a Borno

Sojojin  Nijeriya karkashin dakarun rundunar OPERATON HADIN KAI sun sami nasarar kubutar da yara mata 12 da mayakan kungiyar boko haram suka yi garkuwa da su a kauyen Mussa dake karamar hukumar Askira/Uba dake jihar Borno a Arewa aso gabashin Nijeriya.

Mayakan boko haram sun yi garkuwa da yaran ne a lokacin da suke girbe amfanin gonarsu a ranar 23 ga watan Nuwamba, wanda kuma suka shaki iskan ‘yanci a ranar 29 ga watan na Nuwamba bayan abinda dakarun sojin suka bayyana samun bayanan sirri da kuma ayyukan kakkabe matsalar tsaro a yakin kudancin jihar.

Ta cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta aikewa PRNigeria ta bayyana cewa wadanda aka kubutar din dake mata ne kuma suna karbar kulawar likitoci domin tallafawa lfiyarsu kamar yadda ya kamata. Wanda nan ba da jimawa ba za’a sadasu da iyalansu.

Yaran da aka kubutar suna hadar da  Fatima Shaibu (17), Fatima Umaru (15), Hauwa Abubakar (18), Saliha Muhammed (15), Sadiya Umaru (17), Amira Babel (15), Zara Adamu (17), Nana Shaibu (15), Zainab Musa (18), Zainab Muhammed (17), Jamila Saidu (15), and Hauwa Hamidu (17).

Rundunar Sojin ta yabawa dakarun nata bisa namijin kokarin da uke nunawa a yaki da matsalar tsaro a yankin, sannan ta bukaci Al’ummar dake jihar su sake sanya idanu gami da taimakawa jami’an tsar da bayanan sirri.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com