Hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce arzikin da Najeriya ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ƙara da kashi 3.98 cikin 100 a rubu’i na uku na shekarar 2025.
Cikin rahoton da ta fitar, NBS arzikin cikin gida da Najeriya ta samu a watannin rubu’i na uku na shekarar ya zarta wanda ta samu a daidai wannan lokacin na shekarar 2024.
NBS ta ce fannin noma ne kan gaba a samar da arzikin da kashi 3.79 sai harkar masana’antu da ya ƙaru da kashi 3.77.
A baya-bayan nan dai ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, kamar yadda hukumar ta NBS ke fitarwa, wani abu da gwamnatin ƙasar ke dangantawa da matakan inganta tattalin arziki da take ɗauka.











