Gwamnatin jihar Kano ta sanar da jaddada aiwatar da dokar hana sana’ar achaɓa ta shekarar 2013, wani mataki da ta ce zai taimaka wajen kare tsaro da rage laifuka, da tabbatar da doka da oda a fadin jihar.
Ma’aikatar Shari’a ta bayyana cewa dokar, wadda ta dade tana nan daram kuma za a ci gaba da aiwatar da ita sosai.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da babban mai bai wa gwamnan jihar Shawara Kan Harkokin Labarai na Ma’aikatar Shari’a ya fitar
Babban lauyan jiharkuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya buƙaci jama’a musamman masu baburan haya wata acaɓa da su yi biyayya ga tanade-tanaden dokar.
Ya tunatar da cewa “Dokar ba sabuwa ba ce, kuma dole a kiyaye ta domin amfanin kowa da kowa.”
A cewarsa, gwamnatin jihar ba za ta lamunci karya dokar ba, musamman a yankunan da aka haramta acaɓa.
Dokar ta hana achaɓa a cikin wasu muhimman ƙananan hukumomin birnin da suka haɗa da Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo (Jido), Dawakin Kudu (Tamburawa, Gurjiya da Jido Ward), Fagge da Kumbotso.
Haka kuma, dokar ta tanadi hukunci mai tsauri ga masu karya ta, wanda ya haɗa da ɗaurin watanni shida, tara na Naira 10,000 da kuma yiwuwar ƙwace babur gaba ɗaya.
Ga direbobin da ke aiki a yankunan da aka amince da yin achaɓa, gwamnatin ta nanata wajabcin yin rajista da mai unguwa da sashen ayyuka na ƙaramar hukuma da kuma DPO na yankin su.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga direbobi da fasinjoji da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin sufuri da su tabbatar da cikakken bin dokar.











