Home Labarai Ministan Tsaro Badaru Abubakar ya yi murabus

Ministan Tsaro Badaru Abubakar ya yi murabus

Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take, yana mai bayyana dalilan lafiya a matsayin abin da ya tilasta masa yin hakan.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da maitamaka shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar wadda ta ce a cikin  wata wasika mai dauke da kwana watan 1 ga Disamba, wadda aka aika wa Shugaba Bola Tinubu, tsohon ministan ya ce dole ne ya bar kujerar don kula da lafiyarsa. Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin nasa tare da yaba masa kan hidimar da ya yi wa ƙasa.

Ana sa ran Shugaban Ƙasa zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru cikin mako mai zuwa.

Badaru Abubakar, mai shekaru 63, ya yi gwamna a Jihar Jigawa na zango biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin a naɗa shi Ministan Tsaro a ranar 21 ga Agusta, 2023.

Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin ƙasa, inda ake jiran ƙarin bayani kan matakan da gwamnati za ta dauka nan gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp