Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take, yana mai bayyana dalilan lafiya a matsayin abin da ya tilasta masa yin hakan.
Read Also:
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da maitamaka shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar wadda ta ce a cikin wata wasika mai dauke da kwana watan 1 ga Disamba, wadda aka aika wa Shugaba Bola Tinubu, tsohon ministan ya ce dole ne ya bar kujerar don kula da lafiyarsa. Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin nasa tare da yaba masa kan hidimar da ya yi wa ƙasa.
Ana sa ran Shugaban Ƙasa zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru cikin mako mai zuwa.
Badaru Abubakar, mai shekaru 63, ya yi gwamna a Jihar Jigawa na zango biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin a naɗa shi Ministan Tsaro a ranar 21 ga Agusta, 2023.
Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin ƙasa, inda ake jiran ƙarin bayani kan matakan da gwamnati za ta dauka nan gaba.











