Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro.
Zaman majalisar ya cika da ruɗani a yau Laraba yayin da wasu ‘yanmajalisar ke cewa janar ɗin, wanda shi ne tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, ya rusuna ya wuce ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba, da kuma waɗanda suka ce dole sai ya amsa.
Daga ƙarshe dai Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya shawo kan hayaniyar kuma ya amince cewa akwai buƙatar Janar Musa mai ritaya ya amsa tambayoyin da suka dace.
Da yake jawabi, janar ɗin ya bayyana shirinsa na shawo kan matsalar tsaro, da kuma dawo da martabar rundunar sojin ƙasar a idon ‘yan Najeriya.
“Wannan ba lokaci ne na yin siyasar “rusuna ka wuce ba”. Hatta Donald Trump yana matsa mana. Ba game-garin mutum ba ne, tsohon babban hafsan tsaro ne,” kamar yadda Akpabio ya bayyana lokacin da ya miƙe daga kujerarsa lokacin da ake hayaniyar.
Ana sa ran Janar Musa zai fara aiki nan take bayan Mohammed Badaru ya sauka daga muƙamin a ranar Litinin.









