Rahotanni na bayyana cewa masu bauta 38 da aka sace a cocin Kwara da ke ƙaramar hukumar Eruku a ranar 18 ga Nuwamba, 2025, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku tare da jikkatar wani sun koma gida lafiya bayan an kubutar da su.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Dada Sunday ya fitar a daren Talata, ya tabbatar da cewa gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya miƙa waɗanda aka ceto ga shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Honourable Awelewa Olawale Gabriel, a birnin Ilorin.
Da yake karɓar wadanda aka ceto, Awelewa ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamna AbdulRazaq da duka hukumomin tsaro bisa gaggawa da ƙoƙari wajen ceton mutanen.
Ya ce aikin haɗin gwiwar jami’an tsaro da gwamnati ya taimaka wajen kammala ceto cikin lokaci, tare da ba wa wanɗanda aka kuutar cikakkiyar kulawa.
Sanarwar ta ce tawagar waɗanda aka ceto ta isa garin Eruku da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Talata, inda dangi da mazauna yankin suka tarbe su cikin murna da farin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati za ta ci gaba da bai wa tsaro mahimmanci, tare da ƙarfafa matakan kare rayuka da dukiyoyi a dukkan gundumomi 10 na yankin.









