Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ceto ɗalibai 100 daga cikin mutum 315 da ’yan bindiga suka sace a Makarantar St. Mary’s da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja.
’Yan bindigar sun kai farmakin ne a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, inda suka mamaye makarantar suka tafi da mutum 315 da suka haɗa ɗalibai 303 da malamai 12.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro tare da mafarauta na yankin sun bazama cikin dazuzzukan da ke makwabtaka da Papiri domin neman waɗanda aka sace.
A rana ta farko bayan harin, yara 50 sun yi nasarar tserewa kuma suka koma hannun iyalansu lamarin da ya kawo addadin waɗanda suka rage a hannun ƴan bindigar zuwa mutum 265 kafin wannan sabon cigaba na ceto wasu daga cikinsu.
Gwamnatin Jihar dai ta bayyana cewa kafin aukuwar lamarin ta samu sahihan bayanan sirri game da yiwuwar tashin hankula a sassan Neja ta Arewa, saboda haka ta dakatar da ayyukan gine-gine tare da rufe makarantu masu kwana a yankunan da abin ya shafa.









