Najeriya ta ce jirgin ta ya yi saukar gaggawa ne a Burkina Faso

Mahukunta a Najeriya sun ce jirgin NAF C-130 da ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal.

Sanarwar da rundunar Sojin saman Najeriya ta fitar ta ce ma’aikatan jirgin sun taso ne daga Legas amma sun lura da wata matsala wanda hakan ya sa aka yi taka-tsan-tsan da sauka a Bobo-Dioulasso na Burkina Faso, filin jirgin sama mafi kusa, lamarin da ya yi daidai ƙa’idojin tsaro da ka’idojin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ma’aikatan rundunar saman Najeriya suna cikin ƙoshin lafiya kuma sun samu kyakkyawar kulawa daga hukumomin da suka karɓi baƙuncinsu, ana ci gaba da shirye-shiryen ci gaba da tafiyar da aikin da suka sanya a gaba.”

Rundunar sojojin saman Najeriya ta yaba da tallafin da aka samu a wannan lokaci tare da tabbatar wa da jama’a cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen bin ƙa’idojin aiki da ƙa’idojin tsaro, tare da tabbatar da kare lafiyar ma’aikatanta yayin da take kiyaye dokikoin da kundin tsarin mulki ya tanada.”

Sai dai da alama labarin Najeriya na yadda lamarin ya auku ya ci karo da matsayin gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso da kuma ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel, waɗanda suka ce jirgin ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ne ba tare da izini ba kuma aka tilasta masa sauka.

Kungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta yi alla-wadai da lamarin a matsayin “ketare sararin samaniyarta da kuma keta ƴancin kasashe mambobinta,” tare da bayyana saukar jirgin a matsayin “aikin rashin abokantaka da aka yi ba tare da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da ƙa’idojin sufurin jiragen sama ba.”

Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar rashin aminta da kuma sauya ƙawance a faɗin yammacin Afirka.

Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne suka kafa Ƙungiyar AES, lamarin da ya sa suka fice daga Ƙungiyar ECOWAS a farkon wannan shekarar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com