Hukumar yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ce za ta yi bincike kan zargin da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi wa shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.
Dangote ya mika ƙorafi ga hukumar ICPC a ranar Talata, inda ya zargi Farouk da cin hanci da rashawa da almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Bayan sa’o’i kaɗan da shigar da ƙorafin, ICPC ta tabbatar da karɓarsa tare da bayyana aniyarta ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar a shafukan sada zumunta na ICPC, ya ce “Hukumar ta karɓi ƙorafin Dangote a hukumance a ranar Talata 16 ga Disamba, 2025, ta hannun lauyansa.”
A cikin ƙorafin, “Dangote ya zargi Farouk da kashe sama da dala miliyan 7 wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu a ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida, ba tare da bayyana sahihiyar hanyar samun kuɗin ba.
Korafin ya ce Farouk ya yi amfani da muƙaminsa a NMDPRA wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin amfanin kansa, lamarin da ya janyo asara ga ’yan Najeriya.
A nasa martanin, shugaban hukumar NMDPRA, Ahmed Farouk, ya ce yana maraba da binciken da hukumar ICPC za ta gudanarwa a kansa.
Ya ce ya yi imanin cewa binciken zai ba da dama a duba lamarin cikin adalci da natsuwa, tare da fayyace gaskiyar al’amura domin wanke sunansa.
Ahmed Farouk ya ƙara da cewa ba zai yi musayar zarge-zarge a bainar jama’a ba yana mai cewa zai bari binciken hukuma ya yi aikinsa yadda ya kamata.








