Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da kudirin hukuncin kisa ga masu garkuwa

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba ta goyon bayan ƙudirin majalisar dattawa na gyara dokar yaƙi da ta’addanci wadda ta ce a riƙa yanke wa masu sace mutane hukuncin kisa.

Wannan na zuwa ne bayan lauyan gwamnati kuma ministan Shari’a na ƙasar, Lateef Fagbemi ya ce bai kamata a riƙa yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ba.

Fagbemi ya nuna damuwa kan yiwuwar cewa ƙasashen duniya za su iya ƙin miƙa wa Najeriya masu laifi bisa dogaro da kauce wa hukuncin kisa da kuma dalilan jin ƙan ɗan’adam.

Ya ce, “Dole ne mu yi la’akari da matsalolin da ke tattare da sanya hukuncin kisa a cikin doka, musamman yadda hakan zai iya kawo cikas ga haɗin gwiwar ƙasashen duniya wajen yaƙi da ta’addanci.”

“Yawancin ƙasashe abokan hulɗarmu za su iya ƙin mika wa Najeriya manyan masu laifi idan suna fuskantar barazanar hukuncin kisa.”

Ministan ya kara da cewa, “Ta hanyar saka wannan hukunci, zai iya samar da mafaka ga manyan masu laifi a ƙasashen waje, domin kotunan ƙasashen waje za su hana a mayar da su Najeriya bisa dalilan kare hakkokin ɗan’adam.”

Ƙudirin dai ya ƙunshi yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ba tare da yiwuwar sassaucin kotu ko tara ba, inda aka fara karantawa a majalisar a ranar 27 ga watan Nuwamba, sai na biyu kuma a ranar 3 ga watan Disamba.

Fagbemi ya bayyana waɗannan hujjoji ne a lokacin taron jin ra’ayin jama’a da majalisar ta shirya tare da haɗin gwiwar kwamitocin haƙƙokin ɗan’adam da Shari’a da tsaro da tattara bayanan sirri, da ma’aikatar cikin gida.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com