Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Haɗin Kai sun samu nasarar kashe ƴanbindiga tare da ceto wasu fararen hula da aka sace a wani samame da suka kai a karamar hukumar Konduga, Jihar Borno.
Sojojin, tare da haɗin gwiwar dakarun ƴan sa kai ta CJTF, sun yaƙi ƴanbindigar ne a kan hanyar Sojiri a safiyar ranar 4 ga Janairu, 2026.
Rundunar ce ta bayyana hakan a shafinta na X.
A yayin samamen, an kashe ƴanbindiga guda biyar yayin da suka ceto mtum 3 da aka sace ba tare da asarar rai daga bangaren sojoji ba.
Haka kuma, sojojin sun ƙwato bindigogi na AK-47 da wasu kayan yaki daban-daban.
Rundunar ta ce wannan aiki ya nuna jajircewar sojojin Najeriya wajen kai farmaki kan ƴanbindiga, yayin da suke mai da hankali wajen kare rayukan fararen hula da tabbatar da tsaro a yankin.











