Ƴansanda sun ɗauke makeken bam ɗin da aka gani a jihar Neja

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Neja ta kwance tare da ɗauke wani makeken bam da aka gani a dajin Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu.

A wata tattaunawa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Mashegu, Umar Igade ya ce bayan samun kiran waya daga ƙauyen Zugurma, cewa an ga wani abu kamar bam a ƙasa “na kira DPO na wannan yanki, inda ya tura jami’an tsaro domin su duba gaskiyar al’amarin.

“Bayan da suka isa wurin sun tabbatar da cewa bam ne. Bam ne mai girma, guda ɗaya.”

A baya-bayan nan an samu rahotanni daga wasu ƙauyuka a arewacin Najeriya kan yadda al’umma suke tsintar abubuwan fashewa, bayan wani hari da Amurka ta kai a ƙarshen watan Disamba kan wani yanki mai fama da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makami.

Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ya ce ya zuwa yanzu ba su da tabbas kan ko wannan bam da aka tsinta na daga cikin waɗanda Amurka ta yi amfani da su wajen kai harin na ranar 25 ga watan Disamba.

Ya ce “jami’an tsaro sun dauki bam din kuma suna kan bincike, saboda haka su ne za su tabbatar mana ko irin bam din da aka gani ne a Sokoto da Kwara waɗanda Amurka ta yi amfani da su wajen kai hari.”

“Masu warware bam sun zo daga Minna, sun kwance shi sun saka shi a mota kuma sun tafi da shi zuwa babban ofishin ƴansanda da ke garin Minna domin ci gaba da bincike,” a cewar Igade.

Neja na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ƴan bindiga wadanda ke kai hare-hare kan ƙauyuka suna kashewa da garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa.

A cikin ƙarshen makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari a ƙauyen Kasuwan Daji da ke jihar ta Neja inda ake zargin sun kashe mutum sama da 40.

Kuma a cikin watannin da suka gabata ƴan bindiga sun kai hari kan ƙauyen Papiri, inda suka yi garkuwa da sama da mutane 200, waɗanda suka hada da ɗalibai da malamai, waɗanda daga baya aka sako su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com