Ku daina kirana da na janye takarar shugabancin kasa a shekarar 2027

Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi kan kiraye-kirayen da ake yi masa na ya ajiye takara a yaƙin neman shugabancin kasa ƙarkashin jam’iyyar haɗaka ta ADC, yana mai cewa hakan cin amanar ‘yan Najeriya ne.

Sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta bayyana cewa duk wani yunkuri na ganin Atiku ya ajiye takara zai goyi bayan manufofin kama-karya ne kawai tare kuma da tauye hakkin dimokuradiyya a Najeriya.

Sanarwar ta ce a cikin shekaru kusan uku da suka gabata, ‘yan Najeriya sun fuskanci wahalhalu masu tsanani sakamakon manufofin tattalin arziƙi a ƙarkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin mayar da siyasar Najeriya ta zama ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ta hanyar raunana jam’iyyun adawa.

Sanarwar ta kara da cewa “Jam’iyyar ADC za ta ci gaba da gudanar da tsarin tsayar da ɗan takararta kuma duk wani matsin lamba daga APC ko masu tsoma baki daga waje ba zai yi tasiri ba saboda ba su da ikon yin zagon ƙasa kan wanda ADC za ta tsayar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com