Home Labarai ICPC za ta ci gaba da binciken shugaban NMDPRA duk da Dangote...

ICPC za ta ci gaba da binciken shugaban NMDPRA duk da Dangote ya janye ƙorafinsa

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike kan tsohon shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA), Farouk Ahmed, duk da cewa attajiri mafi kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya janye ƙorafin da ya shigar a kansa.

Lauyan Dangote, Ogwu Onoja, ne ya aika takardar janye ƙorafin zuwa ga ICPC.

Dangote dai ya buƙaci hukumar ta binciki Ahmed a watan Disamban 2025 kan zargin amfani da muƙaminsa wajen satar kuɗaɗen gwamnati, inda ya ce yana da hujjoji da suka tabbatar da zarginsa.

Sai dai, mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya bayyana cewa duk da janyewar ƙorafin, hukumar za ta ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiya da adalci da kuma yaƙi da cin hanci a Najeriya.

Odey ya ƙara da cewa ci gaba da binciken zai nuna cewa hukumar na yin aikinta ba tare da la’akari da matsayi ko shaharar mutum ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp